Yankin Savannah

Yankin Savannah


Wuri
Map
 9°N 2°W / 9°N 2°W / 9; -2
Ƴantacciyar ƙasaGhana

Babban birni Damongo
Labarin ƙasa
Sun raba iyaka da
Bayanan Tuntuɓa
Lamba ta ISO 3166-2 GH-SV

Yankin Savannah Yana daya daga cikin sabbin yankuna na Ghana kuma duk da haka shine yanki mafi girma a kasar. Kirkirar Yankin ya biyo bayan gabatar da koken da Majalisar Gargajiya ta Gonja, karkashin jagorancin Yagbonwura Tumtumba Boresa Jakpa I. Bayan samun amsoshi masu kyau daga duk masu ruwa da tsaki a Yankin Arewa (yankin da aka balle daga), Hukumar Brobbey (Hukumar da aka dorawa alhakin kirkiro sabbin yankuna), an gudanar da zaben raba gardama a ranar 27 ga Disamban shekarar 2018. Sakamakon ya kasance eh 99.7%. Shugaban Jamhuriyar Ghana ya rattaba hannu tare da gabatar da kayan aikin Tsarin Mulki (CI) 115 ga Yagbonwura a gidan Jubilee, Accra ranar 12 ga Fabrairu 2019. Kaddamarwa ya sami halarta sosai daga 'ya'yan Gonjaland maza da mata ciki har da duk Mps na yanzu da na baya, (MDCEs) da duk masu nadawa tare da asalin Gonjaland. An ayyana Damongo a matsayin babban birnin sabuwar yankin Savannah. Yana a arewacin kasar. An raba Yankin Savannah zuwa gundumomi 7; Bole, Gonja ta tsakiya, Gonja ta Arewa, Gonja ta Gabas, Sawla/Tuna/Kalba, Gonja ta Yamma, Arewa maso Gabashin Gonja da Mazabu 7; Bole/Bamboi, Damongo, Daboya/Mankarigu, Salaga ta Arewa, Salaga ta Kudu, Sawla/Tuna/Kalba da Yapei/Kusawgu.[1][2]

  1. Zoure, Stephen (27 December 2018). "Mahama votes in referendum for proposed Savannah Region in Bole". MyNewsGH. Retrieved 28 December 2018.
  2. "'Savannah will soon catch-up with other regions' - Akufo-Addo assures". Citi Newsroom (in Turanci). 2019-05-20. Retrieved 2019-05-20.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search